Najeriya na murnar ranar Dimokradiyya

Image caption Shugaba Jonathan

A yau ne Gwamnatin Najeriya da ma gwamnatocin Jihohi ke bikin murnar cika shekara guda kan karagar mulki bayan zaben da akayi na shekara ta dubu biyu da goma sha daya.

Sai dai tun bayan da kasar ta koma turbar dimokradiyya a shekarar 1999, wani babban kalubale da take fuskantar ta shine na tabarbarewar sha'anin tsaro wanda kawo yanzu ta kasa shawo kansa.

Matsalar dai bisa dukkan alamu ta fi kamari a baya-bayan nan da ake yawan samun hare-hare na bama-bamai da na bindiga da kuma tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa.

Tabarbarewar tsaron dai na shafar kasuwanci a wasu manyan biranen kasar na kuma jawo zulumi da fargaba musamman inda ake yawan kai hare haren.

Karin bayani