Zanga zanga a ranar demokradiya a Najeriya

legas Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zanga zanga a Legas

Daliban jami'ar Legas dake kudancin Najeriya sun gudanar da zanga zanga don nuna rashin jin dadi akan canza sunnan makarantarsu zuwa sunan MKO Abiola.

A cewar daliban matakin bai dace ba duk da cewar suna mutunta margayi MKO Abiola wanda ake kallo a matsayin wani jigo a siyasar kasar kuma daga wannan yankin na kudancin Najeriya ne ya fito.

A ranar Talata ne Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya gabatar da jawabi ga 'yan kasar game da bikin cika shekaru goma sha uku da komawar kasar kan tafarkin mulkin demokradiya ba kakkautawa.

Wanda kuma shine shekara guda bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban kasar.

Shugaba Jonathan ya tabo batutuwa da dama a cikin jawabin, da suka shafi tsaro da noma da tattalin arziki da kuma wutar lantarki.

A cikin jawabinne, Shugaba Jonathan ya bada umurni cewar a sauya sunan Jami'ar Legas ya koma sunan Cif MKO Abiola.

Karin bayani