Sudan ta janye sojojin ta daga Abyei

Sawarmi sojan Sudan

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Sawarmi sojan Sudan

Kasar Sudan ta bayar da sanarwa cewar ta janye sojojin ta daga yankin Abyei wanda ake takaddama a kansa dake kan iyakar ta da Sudan ta kudu.

Wannan matakin ya zo ne kafin a fara tattaunawar sulhu tsakanin kasashen biyu a kasar Ethiopia.

Kasashen biyu sun kusa shiga yaki sosai bayan da Sudan ta kudu ta mamaye kauyen Heglig mai arzikin man fetur da cewa yankin ta ne.

Wannan ya jawo rikici tsakanin kasashen biyu a kan iyakar, daga bisani sudan ta kwace yankin mai arzikin man fetur.