Wasu kasashen Turai sun kori jakadan Syria

syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wadanda aka kashe a garin Houla na Syria

Wasu kasashen Turai sun kori jakadan kasar Syria dake kasashen su, inda suke ci gaba da kakkausar suka na kisan gillar fiye da mutane dari wadanda galibinsu kananan yara ne a garin Houla na kasar Syria.

Kasashen Amurka da Burtaniya da Faransa da Jamus da Spain da Italiya hade da kasashen Australia da Canada duk suma suna bin sahun wajen daukar irin wannan mataki.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake kula da kare hakkin bil'adama, ya ce binciken daya gudanar kan kashe kashen da aka yi a garin Houla na kasar Syria, ya nuna cewa akasarin wadanda aka kashe an yi musu kisar gilla ne.

Wani kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya ce masu sa ido na Majalisar wadanda yanzu haka suke kasar Syria, sun gano cewa kasa da mutane 20 ne aka harbe su da bindiga daga cikin mutane fiye da 100 da aka kashe.

Ya kara da cewa wasu shaidu sun zargi 'yan bindiga dake goyon bayan gwamnati ne da wannan danyen aiki, inda Majalisar ta ce kashe kashen musamman na 'kananan yara wani babban laifi ne da aka aikata akan bil'adama.

Karin bayani