Girgizar kasa ta hallaka mutane 16 a Italiya

Hakkin mallakar hoto evn
Image caption Italiya

Wata girgizar kasa da aka yi a arewacin Italy ta hallaka mutane goma sha shida, akwai kuma mutum guda da har yanzu ba a gan shi ba.

Girgizar kasar ta faru ne kusa da Modena dab da wani yanki da aka yi wata girgizar kasar kwanaki tara da suka gabata.

Masana'antu da manyan shagunan ajiye kayayyaki sun ruguje suka afka wa ma'aikata, haka kuma coci-coci sun rushe.

Wani tarkace da ya fado ya hallaka wani Pada dake kokarin ceton mutum-mutumin Mary.

Karin bayani