Za a kare farar hula a kai hari kan AlQaeda

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barack Obama

An ba da rahoton cewa Shugaba Obama na Amurka da kansa ya amince da a yi amfani da jiragen yaki masu sarrafa kansu wajen mayar da martani kan kowanne hari da 'yan gwagwarmaya na Al-Qaeda suka kai.

Rahoton da jaridar Newyork Times ta bayar ya ce, an gabatar wa Mr Obama jerin mutanen da ake harin kashewa aka kuma nace kan lallai sai ya nuna goyon bayansa ga shirin.

Wannan shiri dai wani babban sirri ne, to amma Fadar gwamnatin Amurkar White House ta ba da tabbacin cewa Shugaban kasar ya dauki wasu matakai na kauce wa kai harin a kan farar hula.

Jiragen Yakin da ba su da matuka za a tura su ne yankunan da ake zargin akwai 'yan kungiyar ta al-Qaeda a kasashen Yemen da Somalia da kuma Pakistan.

Karin bayani