Za a mikawa Palastinawa gawar mutane sama da 90

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mahmoud Abbas

Nan gaba a yau ne za a mika wa hukumar Palasdinawa gawar mutane fiye da casa'in wadanda aka kashe a lokacinda suke kai hare-hare a kan Isra'ila.

Isra'ilar ta ce wannan wani karimci ne na amintaka.

Gawarwakin dai sun hada da na 'yan kunar bakin-wake da sojin sa kai wadanda suka rasa rayukkansu lokacinda suke yunkurin kai harin tun daga shekarar 1975.

Za a yi wani taro na musamman na karbar gawarwakin a garin Ramallah.

Palasdinawan dai na kallon mutanen da suka rasa rayukkan su a matsayin shahidai a yayinda Isra'ila ke kiran su 'yan ta'adda.

Mika gawarwakin wani bangare ne na yarjejeniyar da aka cimma cikin wannan watan don kawo karshen yajin cin abinci da daruruwan fursunonin palasdinawa ke yi a gidajen Yarin Isra'ila.

Karin bayani