Yan tawaye a Syria sun bai wa gwamnati wa'adi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojan Syria

Kungiyar 'yan tawayen Syria ta gitta wa gwamnati wa'adin kwanaki biyu ta janye dukkan sojojin ta daga birane da Kauyuka, in ba haka ba kuma za ta yi watsi da duk wani abu da ya jibanci shirin zaman lafiyar.

A wani faifan vidio da suka tura ta yanar gizo, wani jami'i na kungiyar 'yan tawayen ya bayyana cewar idan gwamnatin ba ta yi aiki da wannan sharadi ba zuwa tsakiyar ranar Jumma'a, to babu wani dalili da zai sa mayakan 'yan tawayen su yi aiki da yarjejeniyar zaman lafiyar.

'yan tawayen suka ce dole ne gwamnatin ta kiyaye da sharuddan zaman lafiyar da wakilin hadin-gwiwa na Larabawa da Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan ya tsara.

Kuma acewar yan tawayen dole ne gwamnatin ta shiga tattaunawa da Majalisar Dinkin Duniya kan mika mulki ga alumma.

Karin bayani