Matsalar wariyar launin fata a Ukraine

Nuna wariyar launin fata a Ukraine
Image caption Nuna wariyar launin fata a Ukraine

Shugaban Ukraine, Viktor Yanukovich, ya fadawa BBC cewa gwamnatinsa ba za ta kyale masu tada hankali a filin wasan kwallon kafa , su kawo cikas ga gasar cin kopin kasashen Turai da za'a yi a watan gobe a Ukraine din da kuma Poland.

Ya ce jami'an tsaron kasar za su kasance cikin shirin ko ta kwana domin maida martani cikin sauri ga duk wata fitina, amma ya ce irin wadannan masu tada fitini ba su yawa da Ukraine, idan aka kwatanta da sauran kasashe.

A farkon wannan makon ne dai, wani rahoton BBC ya yi zargin cewa matsalar wariyar launin fata ta yi kamari a kasar ta Ukraine, kuma za'a iya cin zarafin 'yan wasa da ma'abota wasan kwallon kafa bakar fata da na Asiya.

Karin bayani