Masu hada-hadar jiragen sama sun bukaci a rufe filin jirgin saman Abuja

Kungiyar masu Kamfanonin jiragen sama a Najeriya sun bukaci hukumomi da su rufe babban filin jirgin sama na Abuja, fadar gwamnatin kasar, saboda matsalolin da suka danganci samar da wutar lantarki.

Wani jami'in kungiyar kamfanonin jiragen saman ya shaidawa BBC cewa kamata ya yi a rufe filin jirgin saman na Abuja har sai an magance matsalar saboda rayuwar fasinjoji na cikin hadari.

Sai dai wani jami'in a mai'akatar zirga-zirgar jiragen saman kasar ya shaidawa BBC cewa matsalar bata kai a rufe rufe filin saukar jirgin saman ba saboda ana gyare gyare kuma kwananan za a kammala.

A farkon wannan watan wani jirgin sama ya fado a birnin Legas, inda ya hallaka mutane fiye da dari da hamsin.