Amurka ta kashe wani Jagoran Al-ka'ida

Hakkin mallakar hoto AFP

Amurka ta ce ta kashe jagoran Al-ka'ida na biyu a wani harin jirgin sama mara matuki da ta kai a Pakistan.

Manyan jami'an kasar ta Amurka sun bayyana Abu Yahaya da cewa yana cikin jagororin kungioyar da suka fi kwarewa.

Amurka tace mutumin ya taka muhimmiyar rawa a hare-haren da kungiyar ke kaiwa kan cibiyoyin kasashen Yamma.

Tun da farko ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta kira karamin jakadan Amurkar, Richard Hoagland don ta nuna rashin amincewarta da hare-haren jirage marasa matuka a yankunan kabilu na kasar.

An kashe akalla mutane goma sha biyar ranar Litinin a hari na uku irin wannan a cikin kwanaki uku.

Karin bayani