An yi asarar rayuka a rikicin kabilanci a Nasarawa

jami'an tsaro a Nijeriya
Image caption jami'an tsaro a Nijeriya

Rahotanni daga Jihar Nasarawa a Nijeriya na cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a wani fadan kabilanci da ya barke da safiyar yau a garin Assakio, tsakanin kabilun Madah da Arago game da filin noma.

Daya daga cikin kabilun na korafin cewa an bukaci su rika biyan wasu kudade ne kafin su yi noma, a wani wuri mai dausayi.

Wasu bayanai dai na cewa mutane fiye da talatin ne suka rasa rayukansu, kuma an kona akasarin gidaje dake garin, amma dai an tura jami'an tsaro domin tabbatar da doka da oda.

Wani jami'in gwamnatin Jihar Nasarawar na cewa a yanzu an shawo kan wannan rikici.

A baya dai hukumomin jihar kan shirya taro tsakanin kabilu a kokarin kauce ma irin wadannan tashe tashen hankula, da kan haddasa asarar rayuka, amma bisa dukkan alamu har yanzu ba a samo bakin zaren warware irin wannan rikici ba.

Karin bayani