An yi taro kan rikicin kasar Syria

Tashin hankali a kasar Syria
Image caption Tashin hankali a kasar Syria

Rasha da Jamus sun amince da juna akan bukatar samo hanyoyin siyasa na warware rikicin Syria.

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, wanda ke tsaye tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, a Berlin, baki-dayansu sun amince cewa dole a hana aukuwar yakin basasa a Syriar.

Rasha, daya daga cikin kasashen da suka rage suna goyon bayan Syriar, na fuskantar matsi na cewa ta goyi bayan Majalisar Dinkin Duniya ta dauki tsattsauran mataki akan Syriar.

To amma Moscow ta toshe kokarin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniyar ya sha yi na a yi Allah wadai da Syriar.

Karin bayani