Majalisar Dinkin Duniya za ta kara tallafawa Mali

'Yan gudun hijrar Mali
Image caption 'yan gudun hijirar Mali

Hukumar Kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ninka yawan kudin da aka yi kiyasin za ta kashe wajen tallafa wa dubban 'yan kasar Mali da rikici da kuma karancin abinci suka raba da muhallansu a kasar har sau hudu.

Kuma hukumar tace a yanzu tana bukatar fiye da Dala miliyan 150 domin bayarda agaji ga 'yan Kasar Malin, wadanda suka kauracewa muhallansu, zuwa ko dai wani Sashe na Kasar, ko kuma a makwabtan Kasashe.

Tun bayan soma wani sabon tawayen 'yan kabilar Azbinawa a arewacin Mali dai a farkon bana, ake cigaba da samun karuwar yawan jama'ar da ke bukatar taimakon.

Yawancin su dai mata ne da kuma kananan yara .