Amurka ta ba yara guragu a Zamfara gudunmuwar kekuna

Image caption Hajiya Amina Audu

Yawancin wadanda suka anfana yara ne guragu daga gidajen masu karamin karfi wadanda ba su da sukunin sanyen kekunan don haka sukan yi rarrafe ne zuwa azuzuwansu.

Tallafin kekunan dai ya fito ne daga Free Wheel Chair Mission, wata kungiyar bayar da tallafi ga guragu dake kasar Amurka.

Hajiya Amina Audu ta zama gurguwa ne tana karama sakamakon hadarin mota, amma dai tayi sa’ar samun damar yin karatu har zuwa matakin digiri na biyu, kuma a yanzu ma aikaciyar gwamnati ce.

Irin wannan gatan da samun ilmi ya kawo mata dai, shine a cewar ta ya sa ta ga cewar babbar gudummuwar da zata iya baiwa takwarorinta guragu da ke tasowa ita ce ta ba su kwarin gwiwar zuwa makaranta.

Wasu daga cikin yaran guragu sun nuna farincikinsu bayan da suka dare saman kekunan da aka rarraba musu a wajen wani takaitaccen biki a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

An dai kafa kungiyar ta Free Wheel Chair Mission a shekara ta 2001 da manufar taimakawa guragu matalauta a koina a duniya, kuma shafin naurar internet na Wikipedia yace ya zuwa yanzu ta aike da kekunan guragu dubu 583 zuwa kasashe 81.