ACF ta nuna bacin rai akan rikicin Nassarawa

clashes Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Tashin hankali a Najeriya

Kungiyar tuntubar Juna ta dattawan Arewa a Najeriya, ACF, ta nuna bacin ranta a bisa rikicin kabilancin da ya barke a jahar Nassarawa, inda kimanin mutane talatin suka rasa rayukansu.

A wata sanarwa da ta raba wa manema labarai, ACF din ta ce tana ganin ya kamata 'yan arewa su kawar da banbance-banbancen dake tsakaninsu don ci gaban kasa.

Rikicin ya barke ne a safiyar Alhamis a garin Assakio, tsakanin kabilun Madah da Arago game da filin noma.

Daya daga cikin kabilun na korafin cewa an bukaci su rika biyan wasu kudade ne kafin su yi noma, a wani wuri mai dausayi.

Wasu bayanai dai na cewa mutane fiye da talatin ne suka rasa rayukansu, kuma an kona akasarin gidaje dake garin, amma dai an tura jami'an tsaro domin tabbatar da doka da oda.

A baya dai hukumomin jihar kan shirya taro tsakanin kabilu a kokarin kaucewa irin wadannan tashe tashen hankula, da kan haddasa asarar rayuka, amma bisa dukkan alamu har yanzu ba a samo bakin zaren warware irin wannan rikici ba.

Karin bayani