Mutane 10 sun mutu a harin da aka kaiwa Coci a Bauchi

boko haram
Image caption Harin kunar bakin wake

Rahotanni daga jihar Bauchi a Najeriya na cewa akalla mutane goma sun rasa rayukansu wasu fiye da talatin kuma suka jikkata a wani harin kunar bakin wake a wata majami'a.

Hukumomin tsaro dai sun bayyana cewa maharin ya tuko wata mota ce zuwa majami'ar ta Harvest Field of Christ church.

Ganu dai suka ce harin ya yi kaca-kaca da bangaren ginin majami'ar, yayin da masu ibada kuma suka yi ta kokarin tserewa lamarin daya haifar da tirmutsitsi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Bauchi, Muhammad Ladan, ya shida mani cewa mutane goma ne suka rasa rayukansu ciki harda dan kunar bakin waken, yayin da wasu fiye da talatin kuma suka samu raunuka.

Kungiyoyin agaji da jami'an tsaro ne dai suka kwashe dimbin mutane da suka samu raunuka zuwa asibiti a garin na Bauchi, inda ake masu magani, kuma babban sakatare na kungiuyar agaji ta Red Cross a jihar, Adamu Abubakar, ya ce mutanen na samun kulawa.

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin amma hukumomi cewa suke yi suna kan bincike.

Karin bayani