Ba bu wanda ya tsira a jirgin saman da ya fadi a Legas

hausa Hakkin mallakar hoto listener
Image caption Fasinjoji 153 ne a cikin jirgin saman

Za'a kwashe kwanaki uku ana zaman makokin mutane fiye da dari da hamsin da suka hallaka a lokacin da jirgin saman da su ke ciki ya fadi a Lagos.

Jirgin saman ya fada a kan wasu gidaje kafin ya kama da wuta.

Ma'aikatan ceto sun kwana a wurin suna aiki.

Dukkanin fasijojin da ke cikin jirgin sun hallaka, kuma an sami mutanen da su ka rasu a kasa sai dai ba'a san yawansu ba.

Jirgin saman, mallakar kamfanin Dana air na kasar India, ya tashi daga Abuja zuwa Lagos.

A watan daya gabata wani jirgin saman Dana Air din da ake kyautata zaton shi ne ya fadi ya sami matsala abin da kuma ya sa ya yi saukar gaggawa a Lagos.

Karin bayani