'Batun Syria ne kan gaba a ajandar Majalisar Dinkin Duniya'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga a Syria

Jakadan China a Majalisar Dinkin Duniya, Li Baodong, ya bayyana abin da ke faruwa a Syria a matsayin babban batun da Kwamitin Sulhu na Majalisar zai fi bai wa muhimmanci.

Yanzu haka dai China ce ke rike da shugabancin Kwamitin.

Mista Li ya yi kira ga dukkan bangarorin rikicin kasar ta Syria su aiwatar da shirin zaman lafiya da wakilin musamman na Mjalisar, Kofi Annan, ke jagoranta

Mista Li ya yi wannan jawabi ne a daidai lokacin da shugaban Rasha, Vladamir Putin, ke yin wata ziyarar aiki a China.

Ana sa ran zai tattauna da takwaransa na China, Hu Jintao, game da hadin kai tsakanin kasashen kan makamashin nukiliya - sai dai batun Syria na kan gaba a ganawar ta su.

Da ma dai China da Rasha suna goyon bayan shirin zaman lafiya na Kofi Annan, amma kuma shirin na fuskantar tarnaki.

Karin bayani