Ferdinand ya nuna goyon bayansa ga Ingila

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rio Ferdinand

Rio Ferdinand ya nuna goyon bayansa ga Ingila gabanin gasar Euro ta bana da za'a fara a ranar juma'a me zuwa.

Wakilinsa ya zargi cocin Ingila Roy Hodgson da rashin mutunta dan wasan saboda sunansa baya cikin jerin sunnayen yan wasan da zasu buga a gasar.

" Zan kasance a cikin wata mashaya domin marawa Ingila baya ! ina kaunar yan wasanmu!" a sakon da Ferdinand ya rubuta a twitter.

Sai dai sanarwar tasa na zuwa ne a dai dai lokacinda John Barnes da David Pleat suka goyi bayan shawarar da cocin Ingila ya yanke.

Shi dai Pleat ya ce kalaman da suka fito daga bakin wakilin Ferdinand basu dace ba ya yinda shi kuwa Barnes cewa ya yi ya kamata a marawa cocin Ingila baya.