'Maganin rage radadi na illa ga 'yan wasa'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tambarin FIFA

Babban Jami'in Kiwon Lafiya na FIFA, Dokta Jiri Dvorak , ya ce 'yan wasan kwallon kafa na manyan kungiyoyi na duniya za su fuskanci hatsarin kamuwa da cututtukan da suka danganci hanta da koda saboda shan magungunan rage kaifin ciwo a lokacin wasanni.

Ya shaida wa BBC cewa kusan kashi arba'in cikin dari na 'yan wasan da suka buga Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa ta Duniya da aka yi a Afurka ta Kudu a shekarar 2010 sun sha magungunan rage radadin ciwo kafin su soma buga kowanne wasa.

A cewarsa, wasu 'yan wasan kan yi amfani da magunguna launi uku a duk lokacin da za su buga wasan, lamarin da ya sanya su cikin kasadar kamuwa da cututtuka da dama.

Masana kiwon lafiya sun ce magungunan kashe kaifin ciwo na da hatsari ga koda musamman ma a lokacin motsa jiki kamar buga kwallo inda kodar kan yi aiki ba kakkautawa.

Dokta Dvorak ya yi matukar damuwa game da yadda ake ci gaba da samun 'yan wasa masu tasowa na yin amfani da magungunan kashe radadi.

Karin bayani