An fara bincike game da hatsarin jirgin da aka yi a Legas

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jirgin da ya yi hatsari a Legas

Hukumar Binciken Hadurran Jiragen Sama ta Najeriya ta ce ta fara bincike game da hatsarin da jirgin sama na kamfanin Dana ya yi a Legas bayan da ta gano akwatin da ake kira 'Black Box' a cikin jirgin.

Akwatin dai yana dauke ne da bayanan abubuwan da suka faru a kowanne jirgin sama, kuma yana iya taimakawa wajen gano musabbabin faruwar hadari.

Shugaban Hukumar, Kyaftin Mukhtar Usman, ya ce ana ci gaba da bincike don gano gawarwakin mutanen da hatsarin ya rutsa da su, yana mai cewa yawancin gawarwakin da aka gano sassan jikin mutane ne kawai.

Hukumomin Bayar da Agaji sun ce a halin yanzu an gano gawawwakin mutane 137 a wajen da aka yi hatsarin jirgin.

Hukumar NEMA mai bayar da agajin gaggawa ta ce ta gano gawar wata mata rungume da jaririnta da suka kone.

Karin bayani