Amurka ta kashe wani jigo na kungiyar Al-Qaeda

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mista Jay Carney

Fadar White House ta ce Amurka ta samu gagarumar nasara a kan kungiyar Al Qaeda ta hanyar kisan mutum na biyu a shugabancin kungiyar, wato Abu Yahya Al Libi a Pakistan.

Wani kakakin Fadar White House, Jay Carney, ya tabbatar da labarin kisan Abu Yahya al-Libi, sai dai bai yi cikakken jawabi dangane da yadda aka yi kisan ba.

Ya ce: ''Jami'an leken asirinmu ne suka ba mu bayanan da ke cewa mutumin, wanda shi ne na biyu a kungiyar Al-Qaeda ya mutu.Ba zan iya tabbatar da yadda ya mutu ba, abin da zan iya cewa kawai shi ne, mutumin shi ne shugaban gudanarwa na kungiyar a yankunan kabilun Pakistan''.

Mista Carney ya kara da cewa wannan shi ne karo na biyu cikin wannan shekara da Amurka ta kashe wani shugaba a kungiyar Al Qaeda.

Ya ce hakan ya nuna cewa kungiyar na daf da rugujewa.

Koda a baya dai an taba kama Abu Yahya Al Libi aka tsare shi a sansanin soja na Bagram amma ya tsere.

Karin bayani