Mazauna Maiduguri sun koka

Rahotanni daga Maiduguri dake Jihar Borno a arewacin Najeriya sun ce an wayi gari da hayaki na tashi a wasu unguwannin birnin.

Wasu mazauna garin sun zargi jami'an rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta JTF da kona gidajen farar hula, abinda ya sa mutanen barin gidajensu.

Sai dai rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta musanta wannan zargi.

A waje daya kuma JTF din ta ce yawan 'ya'yan kungiyar nan ta Jama'atul Ahli Sunna Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram, wadanda ta kashe a wani dauki-ba-dadi tsakaninta da 'yayan kungiyar a birnin Maiduguri a jiya, ya karu.

Karin bayani