Sababbin kashe-kashe a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Syria

'Yan adawa da ke fafutuka a Syria sun ce dakarun gwamnatin kasar sun kashe akalla mutane saba'in da takwas a lardin Hama, abin da suka kira zubar da jinin da ya yi kama da wanda aka yi aka Houla.

A cewar masu fafutukar, sojan-sa-kai da ke goyon bayan gwamnati da kuma dakarun gwamnatin sun kai hari a kan kauyen Quber.

Sun ce an harbe yawancin mutanen ne keke-da-keke, wasu kuma an yanka su ne, wasu kuwa sun mutu ne a cikin gidajen da aka bankawa wuta.

Wani mazaunin kauyen Quber, wanda ya tsira daga harin da aka kai, ya shaida wa BBC cewa bayan sojan-sa kai da ke goyon bayan gwamnatin da kuma dakarun gwamnatin sun fice daga kauyen, ya gano gawarwaki kusan arba'in.

Yunkurin Kofi Annan a Syria

Wadannan sababbin hare-hare na zuwa ne a daidai lokacin da wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Syria, Mista Kofi Annan, zai gabatarwa Majalisar sabon kuduri da a ganinsa zai kawo karshen rikicin da ake yi a kasar ta Syria.

Ma'aikatan jakadanci sun ce sababbin hanyoyin sun hada da yiwuwar samun goyon bayan kasashen da ke marawa gwamnati baya, kamar Russia da Iran, kana a daya bangaren a samu wadanda ke marawa 'yan adawa baya, watau kasashen yammacin duniya da na Larabawa.

Manufar yin hakan ita ce wadannan kasashe su kara matsa-lamba kan bangaren da ya fi jin maganarsu domin ya amince a daina rikici a kasar sannan a fara zaman sasantawa.

Sai dai tuni sabon shirin na Mr Annan ya fara cin karo da matsala, domin Burtaniya da Amurka sun ce bai kamata a sanya Iran a yunkurin magance rikicin Syria ba.

Karin bayani