An yi watsi da barazanar 'yan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AP

Jami'an tsaro a Najeriya sun ce za su ci gaba da yin bakin kokarinsu wajen kare rayukan al'umar kasar daga hare-haren 'yan kungiyar Jama'atu Ahlissunnah Lid da'awati wal jihad, wadda wasu kan kira Boko Haram.

Jami'an tsaron suna maida martani ne ga barazanar da kungiyar ta yi, cewa za ta tsaurara farautar da take ta jami'an gwamnati a kasar.

A jiya ne dai kungiyar ta yi wannan barazanar cikin wata sanarwar da ta fitar ta hannun mai magana da yawunta, Abul-Qaqa.

Jami'an tsaro a Najeriya sun bayyana cewa za su ci gaba da arangama da 'yan kungiyar ta Boko Haram..

Kuma alwashin da kungiyar ta yi na ganin bayansu ba zai sa jikinsu ya yi sanyi ba.

Mai magana da yawun rundunar hadin gwiwa don tabbatar da tsaro da ke Jihar Borno, Kanar Sagir Musa, yace ba gudu ba ja baya waje yakin da gwamnati ke yi wajen kawar da kungiyar.

Karin bayani