Yin auren dole zai zama babban laifi a Ingila

Image caption Firayim Ministan Burtaniya, David Cameron

Auren dole ga mace ko namiji zai zama babban laifi a Ingila, da yankin Wales da kuma arewacin Ireland karkashin tanadin wata doka da gwamnatin Burtaniya za ta bayyana ranar Juma'a.

An kiyasta cewa an yi auren tilas tsakanin dubu biyar da dubu takwas a Ingila.

Lamarin dai ya fi shafar mata 'yan kasa da shekaru ashirin da daya, wasu ma ba su wuce shekaru sha biyar ba.

Auren dolen dai ya fi aukuwa ne tsakanin 'yan asalin kasashen Pakistan, da Bangladesh da kuma India.

Karin bayani