Kwamatin da zai rubuta sabon kundin tsarin mulkin Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban gwamnatin Sojin Masar, Hussein Tantawi

Gwamnatin mulkin soja da kuma jam'iyun siyasar kasar Masar sun amince da ka'idojin da za a bi wajen zabar mambobin kwamatin da zai shatawa kasar sabon kundin tsarin mulki.

Bangarorin biyu dai sun kwashe makonni da dama suna ja-in-ja a kan batun

An dai rushe tsohon kwamatin ne bayan kungiyoyin addini masu sassaucin ra'ayi da ma wadanda ba sa so a hada addini da siyasa sun fice daga kwamatin, suna masu zargin cewa musulmi sun fi yawa a cikinsa.

Sabon tsarin da aka amince da shi dai ya tanadi cewa kwamitin rubuta sabon kundin tsarin mulkin zai kunshi wakilan sojoji, da 'yan sanda, da sashen shari'a da kuma kungiyoyin kwadago, da ma malaman addinin Islama da na Kirista

Tuni dai shugaban Majalisar Mulkin Sojan, Hussein Tantawi, ya bukaci Majalisar Dokoki ta yi zama cikin makon gobe domin zabar 'yan kwamitin rubuta sabon kundin tsarin mulkin.

Karin bayani