Bankunan Spain na bukatar karin jari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jim Yong

Asusun ba da lamuni na duniya yace bankunan kasar Spain na bukatar karin jarin akalla dala biliyan hamsin domin kare su daga durkushewa.

Sanarwar ta Asusun na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran Spain din za ta bukaci tallafin kare bankunanta.

Bankunan dai sun bada dimbin basussukan da ba'a zaton kamfanoni za su iya biya sanadiyyar karyewar darajar gidaje a Spain din.

Yankin Turan dai na kokarin farfado da tattalin arzikin wasu kasashen da ke fama da tabarbarewar tattalin arziki.

Karin bayani