An kashe Dakarun majalisar dinkin duniya 7

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun UN a Ivory coast

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe dakarunta na tabbatar da zaman lafiya guda bakwai a wani kwantan bauna da akayi musu a kusa da iyakar Ivory Coast da Laberiya.

Duka wadanda aka kashe din yan Jamhuriyyar Nijer ne.

Wannan yankin iyakar dai an sha samu farmaki wadanda ake zargin yan sojojin sakai ne na Laberiya da kuma yan tawaye na Ivory Coast wadanda suka tsere daga Ivory coast din bayan da aka kama tsohon shuagaban kasar Laurent Gbagbo a bara.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki Moon ya nuna bacin ransa kan farmakin.

Karin bayani