An hallaka sojojin Nijar a Kot Divuwa

Dakarun MDD a Ivory Coast Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun MDD a Ivory Coast

Ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya a Kot Divuwa sun ce wasu fararan hula na daga cikin wadanda aka hallaka a wani kwantan bauna da akai ranar juma'a, inda aka kashe sojojin Nijar bakwai dake aikin wanzar da zaman lafiya karkashin Majalisar Dinkin Duniya a kasar.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar, Ban Ki-Moon, ya bayyan alhininsa game da kisan, ya kuma yi kira ga mahukuntan Kot Divuwan da su yi duk abunda zasu iya yi don gano wadanda suka aikata kisan, su kuma tabbatar an hukunta su.

Mr Moon ya kuma ce har yanzu sauran dakarun su dake yankin na fuskanatar hadari.

Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Abidjan yace akalla fararan hula takwas ne ake kashe a harin da aka kai a kusa da kan iyakar kasar da Liberia.

Ana danganta sojojin haya daga Liberia da mayakan sakai masu goyon bayan tsohon shugaba Laurent Gbagbo da kai hare hare a yankin.

Karin bayani