Kwararru na bincike kan kisa a Syria

Image caption Qubeir a Syria

Kwararru daga majalisar dinkin duniya na gudanar da bincike don gano hakikanin abinda ya faru a kauyen Qubair na kasar Syria, inda wasu 'yan bindiga magoya bayan gwamnati su ka yi kisan gilla.

Masu fafutuka sun ce an kashe mata da kanan yara da dama a kauyen yayin da gwamnati ke cewa wasu 'yan ta'adda ne suka kashe mutane tara.

Garuruwan da rikicin Syriar yafi kamari na cikin wani hali na ha'ulai bisa fargabar farmaki da bukatar kayan agaji.

Kungira bada agaji ta Red Croos dai ta ce mutane miliyan daya da rabi ne ke bukatar kayan agaji a kasar.

Karin bayani