An yi hadarin jirgin sama a Kenya

Shugaban kasar Kenya da Praministansa Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Shugaban kasar Kenya da Praministansa

Wani jirgi mai saukar ungulu dauke da ministan tsaron cikin gidan Kenya, George Saitoti, da wasu mutane biyar ya fadi a wani tsauni, kuma dukkanin wadanda ke jirgin sun rasu.

Helikwaftan ya fa di ne a cikin dajin Ngong dake wajen birnin Nairobi.

Mr Saitoti ya rike mukaman mataimakin shugaban kasa da ministan kudi a karkashin tsohon shugaban kasar Kenyan, Daniel Arap Moi.

Ba'a dai gano musabbabin faduwar jirgin ba, amma wani kakakin gwamnatin Kenyan, Alfred Mutua ya ce babu wata alama dake nuna cewa wata makarkashiya ce ko an kitsa ne da gangan.

Shugaba Mwai Kibaki yace lamarin babban rashi ne ga kasar. Mista Saitoti ya taba zama ministan kudi kuma yayi mataimakin shugaban kasa a zamanin tsohon shugaba Daniel Arap Moi

Karin bayani