An kai hare-hare biyu a wasu coci-coci a Najeriya

Hari kan wani coci-coci a Najeriya Hakkin mallakar hoto s
Image caption Hari kan wani coci-coci a Najeriya

An kai hare-hare biyu a wasu coci-coci a Najeriya. Wasu 'yan bindiga sun bude wuta akan wani coci a karamar hukumar Biu dake arewacin kasar inda suka kashe wata mata.

Wani da ya ganewa idanunsa abin da ya faru ya ce harin ya rutsa da mutane da dama a lokacin da suke ibada a cikin cocin.

A daya bangaran kuma an kai wani harin kunar bakin wake a wata majami'a a garin Jos, babban birnin Jihar Filato inda daga bisani kuma matasa a yankin suka tada tarzoma domin nuna rashin jin dadinsu da harin.

Wasu Karin mutane biyu dai sun rasa rayukansu, amma hukumomin tsaro sun ce kawo yanzu ba za su iya tantance ko harin bam din ne ya yi sanadiyar mutuwarsu ko kuma tarzomar matasan ce ta yi sanadiyar mutuwarsu ba.

Kawo yanzu babu bayanai daga hukumomin kasar akan adadain wadanda suka mutu ko suka jikkata a gaba daya hare haran biyu.

Kuma babu wasu, ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai hare haren

Karin bayani