Matasa sun yi zanga zanga a Jos

An kai hare hare a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kai hare hare a Najeriya

Kungiyar agaji ta Red Cross a Najeriya ta ce wasu gungun matasa da suka yi zanga zanga dazu sun hallaka mutane shida cikin fushi, bayan wani dan kunar bakin wake ya tada wani bam a wani coci a garin Jos dake arewacin kasar.

Matasan sunyi zanga zanga akan tituna bayan wani dan kunar bakin wake ya jikkata akalla mutane 50.

A wani lamarin kuma wasu 'yan bindiga sun bude wuta akan wani coci a kauyen Tabra a jihar Borno lokacinda masu ibada ke addu'i'i a cocin.

Wata mata ta rasa ranta a harin.

Yanzu haka dai kungiyar Jama'atu Ahli sunna Lidda'awati wal jihad da aka fi sa ni da Boko Haram ta yi ikirarin kai hare haran biyu.

Karin bayani