Bankunan Spain na bukatar ceto

Praministan Spain Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Praministan Spain

Praministan Spain, Mariano Rajoy, yayi maraba da yarjejeniyar da ministaocin kudin kasashen turai suka cimma ta rantawa bankunan Spain dala biliyan dari da ashirin da biyar.

Mista Rajoy ya ce yarjejeniyar tana da muhinmanci don zata tabbatar da ci gaba da amfani da kudin bai daya na EURO.

Sai dai ba dukkan 'yan kasar ba ne suka yi marhabin da wannan yarjejeniyar ba.

Wannan mataki dai zai tamakawa iyalai da ma harkokin kasuwanci.

Haka kuma zai farfado da tattalin arzukin kasar ta Spain tare da maido da martabarta ta fuskar basuka.

Karin bayani