An kusa kammala zabe kan kudin Euro a Girka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Girka

An shiga mako na karshe na yakin neman zabe a kasar Girka, wanda sakamakonsa zai nuna ko kasar za ta cigaba da amfani da kudin Euro ko kuma a'a.

Alamu na nuna Jam'iyyar Syriza mai adawa da tsuke bakin aljihun gwamnati da sauran kasashe masu amfani da Euro suka bukata, za ta yi zarra a zaben.

Sai dai sauran jam'iyyu na gargadin nasarar Syriza za ta sa Girka daina amfani da kudin Euro.

Wakilin BBC yace a baiyane take babu wata jam'iyya guda da za ta iya samun nasarar kafa gwamnati ita kadai, abinda ke jawo fargabar Girka za ta sake gaza kafa sabuwar gwamnati bayan wannan zaben.

Karin bayani