Shugaban Nijar ya koka kan rikicin Mali

Shugaba Muhammadou Issoufou na Nijar
Image caption Shugaba Muhammadou Issoufou na Nijar

Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar ya ce kasashen Yammacin Afirka za su nemi izini daga Majalisar Dinkin Duniya su yi amfani da karfin soji a Mali, kasar da ya ce ta zama barazana ga tsaron duniya.

Ya ce kasar ta zama barazana ga duniya mai bukatar amsa a matakin kasa-da-kasa.

Ya ce hakan ya sa kungiyar ECOWAS ta yanke shawarar mika wannan tambaya ga kwamitin sulhu don ya nemo magani, ciki har da matakin soji, wanda a shirye ECOWAS ta ke ta aiwatar da taimakon manyan kasashen duniya irinsu Faransa da Amurka.

Shugaba Issoufou ya furta wadannan kalamai ne a Faransa, bayan wata tattaunawa da Shugaba Francois Hollande.

Mista Hollande ya ce a shirye Faransa ta ke ta goyi bayan matakin sojin da za a dauka a Mali, amma a karkashin jagorancin kungiyar ECOWAS.

Karin bayani