Moon ya damu kan tsanantar rikicin Syria

Hakkin mallakar hoto UN
Image caption Ban ki Moon

Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya, Ban Ki-moon ya baiyana damuwarsa kan abinda ya kira tsanantar rikici a kasar Syria a baya-bayan nan.

Mr Ban ya yi tur da luguden wutar da dakarun gwamnati ke yi a cikin garuruwa da kuma harbi daga jiragen helicopter.

Sai dai yace jami'an sa ido na majalisar na shaida irin hare-haren da 'yan adawar ke kai wa dakarun gwamnati.

Mr Ban din dai ya bukaci bangarorin biyu su yi aiki da dokokin kasa da kasa.

Karin bayani