An baiwa jami'an 'Civil Defence' makamai a Najeriya

arms Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Makamai a Najeriya

Runduna ta daya ta sojojin Najeriya dake Kaduna ta mikawa rundunar jami'an tsaron kare fararen hula,wato civil defence corps makamai domin inganta tsaro a kasar.

Baiwa jami'an makaman dai ya biyo bayan umurnin da gwamnatin tarayyar kasar ta bayar ne na baiwa jami'an makamai bayan da suka shafe shekaru suna gudanar da ayyukansu da gora kawai.

Sai dai kuma wannan mataki na cike da cece kuce, saboda wasu na ganin ba su makamai abu ne da bai dace ba, ganin cewar koda su kansu jami'an tsaro na kasar a kan zarge su da amfani da makamai ba kan ka'ida ba.

Jami'an na Civil Defence Corps sun ce za suyi amfani da makaman yadda suka dace.

An basu bindigogi da harsashai da kuma wasu abubuwan tsaro.

Karin bayani