Shugaba Issoufou na ci gaba da ziyara a Birtaniya

shugaba Issoufou na Nijar
Image caption shugaba Issoufou na Nijar

A ci gaba da ziyarar aikin da yake yi a Burtaniya, dazu shugaban Jumhuriyar Nijar, Alhaji Mahamadou Isufu ya gabatar da wata lacca a Cibiyar nan dake nazari kan al'ummuran yau da kullum ta Chatham House dake nan London.

Bayan haka ne kuma ya yi wata ganawa da Praministan Birtaniya, David Cameron.

A cikin laccar tasa shugaban Mahamadou Isufu ya ce bisa hasashen da bankin duniya da kuma Hukumar bada lamani ta duniya, IMF suka yi, tattalin arzikin Nijar zai bunkasa da kashi 15 cikin 100 a bana, abin da zai sa ya kasance daya daga cikin mafi bunkasa cikin sauri a duniya.

Sai dai ba kowa ne ya ga amfanin wannan habbaka ba saboda fatara da kuma matsalar abinci sun ci gaba da addabar kasar.

Ziyarar dai ita ce ta farko irinta tun shekarar 1969

A jiya ya gana da 'yan Nijar mazauna Birtaniya.

Ranar Alhamis kuma ake sa ran za a yi wata ganawa tsakaninsa da wasu 'yan kasuwa na Birtaniya da Amurka.

Karin bayani