Ana yakin basasa a Syria - Ladsous

Herve Ladsous Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'in Majalisar Dinkin Duniya, Herve Ladsous.

Jami'in da ke kula da al'amuran kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, Herve Ladsous, ya ce a yanzu za a iya daukar rikicin Syria a matsayin yakin basasa.

Wannan ne dai karo na farko da wani jami'in majalisar ya bayyana irin wannan ra'ayi a hukumance.

Mista Ladsous ya ce, a zahiri yankuna da dama a wasu daga cikin biranen kasar sun kubuce daga hannun gwamnati sun koma hannun 'yan tawaye, sannan kuma an samu kaeruwar tashe-tashen hankula matuka.

Wakiliyar BBC ta ce "wadannan kalamai sun biyo bayan wata sanarwa ce ta sakatare janar na Majalisar wanda ya nuna damuwa matuka da yadda tashe-tashen hankula suka kara munana a kasar ta Syria".

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta ce tabarbarewar yanayi a Syria ta sa aikin ceton al'umma ba zai yiwu ba.

Karin bayani