Ana kashe kananan yara a yakin Syria,

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yara a Syria

A karon farko Majalisar Dinkin Duniya ta zayyana sunan dakarun gwamnatin Syria a jerin sunayen masu kashe yara kanana da kuma azabtar dasu.

Jerin sunayen na daga cikin rahoton shekara shekara akan yara a yankin da ake yaki.

Babbar Jami'ar dake kula da yara a fagen yaki Radhika Coomaraswamy, ta shaidawa BBC cewa bata taba ganin yanayin da ba'a kaucewa kananan yara ko ma a far musu kamar irin wannan karon ba.

Wasu daga cikin jerin sunayen rahoton sun hada da masu daukar bindiga daga kasashen Afghanistan da Iraq.

Karin bayani