Kotu tace a rusa majalisar dokokin Masar

Hakkin mallakar hoto AP

Kotun tsarin mulki ta Masar ta yanke hukuncin cewar dole ne a rusa majalisar dokokin kasar sannan a sake sabon zabe.

Kotun ta ce tsarin da aka gudanar da zaben a bara ya saba wa tsarin mulki.

Kotun ta kuma soke wata dokar da ta so hana Ahmed Shafiq -- Pirayim Minista na karshe a karkashin hambararren Shugaban kasa, Hosni Mubarak -- tsayawa takara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da za a yi mako mai zuwa.

Ahmed Shafiq ya yaba da hukuncin, wanda yace wani abin tarihi ne.

Ya ce: "Ya ku mutanen kwarai na Masar, takwarori na 'yan kasa, na tsaya nan gabanku a karshen yakin neman zabe na.

"Lokaci ne da kaddara ta sa ya kasance na tarihi a tarihin Masar".

To amma abokin hamayyarsa na kungiyar 'yan uwa Musulmi, Mohammed Morsi, ya ce bai gamsu ba.

Sai dai kuma ya shedawa wani gidan telebijin da ake kamawa ta tauraron dan Adam cewar yana mutunta hukuncin.

Karin bayani