An kashe mutane 80 a Iraqi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu mutane da suka mutu bayan harin da aka kai a Iraqi

Jami'ai a Iraqi sun ce an kashe akalla mutane tamanin yayin da aka jikkata fiye da 200 a wadansu hare-haren bama-bamai da aka kaddamar a kan 'yan Shi'a a Bagadaza da kudancin kasar.

Bama-baman sun tashi ne a wurare goma a birnin na Bagadaza inda 'yan Shi'a ke taruwa don yin wani biki na addini.

A birnin Hilla na kudancin kasar kuma bama-baman da aka dasa a wasu motoci biyu ne suka tashi, suka kuma kashe akalla mutane goma sha uku, a kofar wani gidan cin abinci da 'yan sanda ke yawan zuwa.

Wani mutum da ya yi rauni aka kuma garzaya da shi asibiti ya bayyana yadda lamarin ya faru:

''Ba zato ba tsammani bom ya tashi a wata mota, sai na fadi kasa, mutane kuma suka yi ta faduwa a kaina''.

Karin bayani