Syria: Amurka ta sake nuna damuwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hillary Clinton, sakatariyar hulda da kasashen wajen Amurka

Amurka ta sake bayyana damuwar ta dangane da makaman da Rasha ke sayar wa kasar Syria.

Sakatariyar Harkokin Wajen kasar, Hilary Clinton, ta cebayanan baya-bayan nan sun nuna cewa Rasha tana kan hanyar kai wasu kananan jiragen yaaki a kasar ta Syria - yunkurin da tace zai kara dagula rikicin na Syria.

Misis Clinton ta yi kalaman ne a wata ganawa da suka yi ta bainar jama'a da shugaban Isra'ila, Shimon Perez.