Ahmed Shafiq zai iya takara a Masar- Kotu

shafiq Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Alon takarar Ahmed Shafiq

Kotun tsarin mulki ta Masar ta yanke hukuncin cewar Pirayi Minista na karshe ga tsohon Shugaban kasa Mubarak, zai iya shiga cikin zagaye na biyu na zaben Shugaban kasar da za a yi mako mai zuwa.

Takarar Ahmed Shafiq dai ta kasance cikin shakku saboda wata dokar da aka bullo da ita a cikin watan Afrilu da ta yi hana wakilan tsohuwar gwamnati tsayawa takara.

Kotun ta yanke hukuncin cewar dokar ta sabawa tsarin mulki.

Ta kuma yanke hukunci cewar kashi daya bisa uku na kujerun majalisar dokoki, wadanda aka yi takara bisa tsarin wanda ya samu mafi yawan kuri'u shi ya yi nasara, ba sa kan ka'ida.

Wakilin BBC a Alkahira ya ce galibin kujerun da ake batu dai kungiyar 'yan uwa Musulmi ce ta lashe su.

Karin bayani