Ana taro a London akan zuba jari a Nijer

issoufou
Bayanan hoto,

hugaban jumhuriyar Nijar, Alhaji Muhammadu Isoufou

Shugaban kasar Nijar, Alhaji Mahamadu Isufu da wasu manyan jami'an gwamnatinsa na tattaunawa a wani babban taro kan batun saka jari a kasar, wanda ake yi a London.

Biritaniya da Amurka ne suka shirya tare da hadin gwiwar kasar ta Nijar.

Haka kuma, 'yan kasuwa da shugabannin kamfanonin Nijar din da kuma wakilan kamfanonin kasashen waje da dama ne ke halartar taron.

An dai shirya taron ne da nufin kwadaita wa kamfanonin kasashen waje Nijar din don saka jari a fannoni da dama, irin su hakar ma'adinai da man fetur da noma da kiwo da sauransu.