Najeriya: majalisa ta kira zaman gaggawa

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, majalisar wakilan kasar za ta gudanar da wani zama na ba zata a gobe Juma'a. A wata sanarwa da akawun majalisar, M. A. Sani-Omolori ya rabawa manema labari a daren jiya, ya bukaci daukacin 'yan Majalisar wakilan da su halarci zaman majalisar da za a fara da misalin karfe 10 na safe.

Ana kyautata zato dai zargin badakalar karbar cin hancin da ake zargin Hon Faruk Lawal ya yi shine batun da zai mamaye tattaunawar da wakilan za su yi.

Wani hamshakin dan kasuwa mai safarar mai, Femi Otedola ne yayi zargin cewa, dan majalisar, Faruk Lawan ya karbi cin hanci dangane da binciken kudaden tallafin da majalisar tayi.

Koda a baya dai majalisar dokokin Najeriya ta sha aukawa cikin badakalar cin hanci da rashawa.