An binne sojojin Nijar bakwai a Yamai

Sojojin Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Nijar

A jamhuriyar Nijar yau ne aka yi jana'izar sojojin nan bakwai da suka rasa rayukansu a kasar Cote D'ivoire makon da ya gabata.

An binne su ne a makabartar musulmi ta Yamai.

A lokacin jawabin da ya gabatar, Praministan Nijar, Briji Rafini ya nuna alhininsa da na kasa baki daya game da mutuwar sojojin, wadanda ya ce sun sadaukar da rayukansu a madadin kasarsu.

Praminista Rafini ya bada sanarwar ba su wasu manyan lambobi na kasa, da kuma yi masu karin girma zuwa mukamai na gaba a soja.

A jiya ne aka kai gawarwakin nasu a kasar kasar ta Nijar cikin wani jirgi na Majalisar Dinkin Duniya.

Sojojin dai sun rasu ne a wani harin kwanton bauna da aka kai masu, yayinda suke sintiri, a ci gaba da aikin tabbatar da zaman lafiya karkashin Majalisar Dinkin Duniyar.

Karin bayani